Labarai

Matar Gwamnan Kebbi Ta Rabawa Mata Kayan Tallafin Sana’o’i

Mai dakin Gwamnan jihar Kebbi, Zainab Nasare Nasir Idris, ta raba kayan tallafin gudanar da sana’o’I ga Mata, a yankin Dole Kaina, da ke karamar hukumar Dandi, a yunkurin da ta ke na ganin matan sun dogara da kansu.

A ya yin bikin bada tallafin, wanda ya gudana, ranar Talata, a garin na Dole Kaina, Matar Gwamnan, ta bayyana matakan da gwamnatin mijin nata, Dr. Nasir Idris ke dauka na tabbatar da walwalar jama’ar jihar, da ma bunkasa rayuwar al’ummar jihar ta Kebbi, tare da bunkasa tattalin arzikinta.

Zainab Nasare, ta kuma jadda yadda shirin na bada tallafi zai zagaya dukkan lunguna da sakunan jihar, tare da kara karfin tattalin arzikin Iyalan da su ka amfana.

Ta kuma kara da rokar wadanda su ka amfana da tallafin, da su kauracewa barnatar da kayyakin da su ka rabauta da su.

Ya yin da a karshe ta roki daukacin al’ummar yankin na Dole Kaina, da Buma da ma sauran wuraren da za a gudanar da zabukan cike gurbi na yan majalissun tarayya, a ranar Asabar mai zuwa, da su fito, su zazzagawa yan takarkarun jam’iyyar APC kuri’a, dan ganin sun samu nasara a zabukan.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button