Labarai

Matar Shugaba Tinubu Ta Bada Tallafin Miliyan 500 Ga Iyalan Da Matsalar Tsaro Ta Shafa

Matar Shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da rabon Naira miliyan 500, a matsayin tallafin Rage-Radadi, da sake neman matsuguni ga Iyalai 500, a jihar Plateau.

An raba kayayyakin tallafin ne dai, a ƙananan hukumomi shida na jihar ta Plateau, da su ka haɗarda: Bassa, Riyom, Barkin-Ladi, Mangu, da Jos ta Kudu, waɗanda faɗace-faɗace da matsalolin rashin tsaro su ka addaba.

Da ta ke bayani, ya yin bikin bada tallafin, ranar Talata, a Jos, Oluremi, ta bayyana cewar, bada tallafin wani ɓangare ne daga cikin Ayyukanta na jinƙan masu ƙaramin ƙarfi, ƙarƙashin shirin RHI, da aka ƙaddamar a watan Yuni, domin inganta rayuwar al’ummar Najeriya.

“Wannan tallafi na kuɗi kimanin Naira 500 na RHI, wani ɓangare ne daga cikin tallafin da mu ke bayarwa, domin sake farfaɗo da rayuwar Iyalai, da ma basu damar sake mallakar muhallai”, a cewarta.

Ta kuma bayyana rashin jindaɗinta, kan halin rashin tsaron da ake ciki a Jihar ta Plateau, wanda ya yi sanadiyyar laƙume rayuka, tare da raba al’umma da dama da muhallansu.

A cewarta dai, wajibi ne a ɗauki ƙwararan matakai, wajen ganin an tallafi waɗanda lamarin ya shafa, wanda kuma shi ne babban abin da Gwamnatin Shugaban ƙasa Tinubu, ta mayar da hankali wajen cimmawa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button