Matasan Bauchi Sun Bawa Majalissa Makonni 2, Domin Janye Dakatarwar Sanata Ningi
Gamayyar matasan jihar Bauchi, da su ka fito daga yankin Bauchi ta tsakiya, sun bawa Majalissar Dattijai ta ƙasa, wa’adin makonni biyu, da ta gaggauta janye matakin da ta ɗauka na dakatar da Sanata Abdul Ningi, ko kuma su maka majalissar a gaban Kotu.
Ƴan Majalissar dai, sun amince da ɗaukar matakin dakatar da Ningi ne, bayan da ya fasa ƙwai kan badaƙalar da ke ƙunshe a kasafin kuɗin 2024, su na masu cewar bayanan nasa tamkar tauye ƴancin majalissar ne, da kuma yi mata ƙazafi.
Sai dai, gamayyar matasan, ƙarƙashin jagorancin Nazeef Abdullahi Rio, sun bayyana ɗaukar matakin dakatar da Ningin a matsayin rashin adalci, tare da roƙon ƴan majalissar da su hukunta Ningi a karan kansa, bisa abinda su ka zarge shi da shi, ba wai rushe wakilcin al’ummar yankin da ya ke wakilta ba – baki ɗaya.
Ka zalika, gamayyar matasan, sun buƙaci da a zurfafa bincike kan lamarin badaƙalar da ake zargi, a cikin kasafin kuɗin.