Zamantakewa

Matashi Ya Hallaka Direban Da Ke Haya Gidansu, Bayan Rikici Kan Filin Ajiye Ababen Hawa

Ana zargin ɗan mai-gidan haya, da hallaka wani Magidanci da ke gudanar da sana’ar tuƙi (Direba), Shonibare Oluwasegun, mai shekaru 36 a duniya, bayan da su ka samu hatsaniya kan filin ajiye ababen hawa, a yankin Ajah, na jihar Lagos.

Wani shaidar gani da ido, ya bayyana cewar, Magidancin mai yara uku, ya dawo gida ne da tsakiyar daren Lahadi, 19 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, ya kuma ajiye motarsa a gaban gidan da ya ke haya, wanda ke lamba 24, Adewunmi Close, Ilaje Ajah.

Bayan ajiye motar ne kuma, sai ya tafi ya kwanta, saboda tsananin gajiyar da ya yi, amma kwanciyarsa ke da wuya, sai ya ji an fara buga ƙofar ɗakin da ya ke, wanda hakan ya tilasta masa katse nannauyan barcin da ya yi awon gaba da shi.

Bayan fitowarsa ne kuma, sai ya ga ashe ɗan mai-gidan da ya ke hayar mai suna, Taiye Adebayo ne ya ke buga masa ɗaki, tare da umartarsa da ya je ya ɗauke motarsa daga inda ya ajiyeta. Nan da nan kuma Oluwasegun ɗin ya fita ya duba, inda ya tabbatar da cewar, a wurin da ya saba ajiye motar tasa dai, a nan ne ya ajiyeta ranar ma.

Daga nan ne kuma rikici ya kaure, inda har ta kai ga Adebayo ɗin ya ɗauko wuƙa ya sokawa Oluwasegun, wanda hakan ne kuma ya yi sanadiyyar rasa ransa.

Shi ma wani ɗan uwa ga mamacin, mai suna Shonibare Oluwasegun, ya bayyana kaɗuwarsa matuƙa game da rasuwar ɗan uwan nasa, inda ya ce da tsakiyar daren Lahadin, misalin ƙarfe 1:29 ya ga an kira da baƙuwar lamba ɗagawarsa ke da wuya kuma, aka sanar da shi batun rasa ran ɗan uwan nasa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button