Zamantakewa

Matashi Ya Hallaka Mahaifiyarsa, A Kano

Wannan al’amari mai ban tsoro ya faru ne, da yammacin Laraba, a Ƙarshen Kwalta, da ke ƙaramar hukumar Ungogon jihar Kano, inda matashin mai suna, Iro Ƙwarangwal ya soka wa uwarsa mai suna, Jummai wuƙa, wanda har ya kai ga rasa ranta, sakamakon saɓanin da su ka samu.

Lamarin dai, ya auku ne, da misalin ƙarfe 5:30 na yammaci.

”Ina tsaye, a ƙofar gidana, sai na ji ihu daga gidan da Matar ta ke,” a cewar wani shaidar gani da ido.

Inda bayan jin ihun ne kuma, sai ya garzaya gidan domin taimakawa, da zuwan sa kuma sai ya tsinci matar da aka sokawa wuƙar kwance cikin jini, ta na kururuwar neman taimako.

Shaidar gani da idon, ya kuma ce wanda ake zargin ya tsere daga wurin da lamarin ya faru, jim kaɗan bayan da zargin jama’a ya juyo kansa, game da hallaka mahaifiyar tasa.

Daga nan ne kuma, aka garzaya da ita Asibiti, a adai-daita sahu, duk jini ya jiƙe mata jiki, a Asibitin ne kuma, Likita ya tabbatar da rasa ranta.

”Tun a jiyan kuma aka binne ta, kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada. Allah ya sanyata a Aljannah,” kamar yadda shaidar ya yi mata Addu’a.

Da aka tuntuɓe shi, Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, tare da alƙawarin yin ƙarin bayani daga baya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button