Zamantakewa

Matashi Ya Shiga Hannu, Bisa Zargin Aikata Fyaɗe, A Masallaci

Rundunar ƴan sandan jihar Yobe, ta kama wani matashi mai suna, Muhammed Audu, mai shekaru 18 a duniya, bisa zargin da laifikin aikata wa wata yarinya mai shekaru 5 kacal a duniya fyaɗe, a ƙauyen Kayeri, da ke ƙaramar hukumar Fune.

Yarinyar da aka aikatawa wannan aika-aika dai, ta raka Yayarta tallen Goro ne, a yankin Kabul, da ke garin na Kayeri, a ranar 30 ga watan Afrilun da ya gabata, inda wannan matashi da ya kasance babban dilan ƙwayoyi ya aike ta ta sayo masa wani abu.

Bayan tafiyar ta ne kuma, sai ya bita a baya, ba tare da sanin ƴar uwarta ba, ya kuma ja ta cikin wani Masallaci da ba a kammala gininsa ba, da ke yankin na Kabul, tare da aikata mata fyaɗe.

A cewar wata majiya dai, wanda ake zargin ya jiwa yarinyar rauni, tare da barinta ta na zubar da jini.

”Da ya ji muryar mutane su na zuwa kusa da inda ya ke aikata mata fyaɗen, ya yi yunƙurin tserewa, amma an yi nasarar cafke shi, tare da tilasta masa bayyana abinda ya aikata”, a cewar majiyar.

Tuni kuma aka miƙa matashin hannun Jami’an ƴan sandan garin Damagum, domin faɗaɗa bincike.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button