Matatar Man Dangote Za Ta Fara Aiki A Watan Oktoba
Matatar Man Dangote, wacce a ke sa ran za ta dinga tace ganga 650,000 na ɗanyen mai, a kowacce rana, za ta karɓi jirgin farko na ɗanyen man da za ta fara tacewa, a wata mai kamawa, kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.
Matatar Man dai, za ta fara samar da sama da ganga 370,000 na Man Diesel, da man Jirgi, daga watan na Oktoba, kamfanin S&P Global Platts, da ya yi shura wajen kawo batutuwan kasuwanci a faɗin duniya ne ya bayyana hakan, ta cikin wani rahoto da ya fitar, a ranar Talata.
Idan mai karatu bai manta ba, a watan Mayun da ya gabata ne, tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da matatar Man, wacce ake kyautata zaton za ta taka gagarumar rawa wajen farfaɗo da fannin mai da iskar gas na ƙasar, tare da bunƙasa tattalin arziƙi.
Tsarin bututun man da aka samar a kamfanin dai, ya kasance mafi girma a faɗin duniya, inda ya shafe sama da tsawon kilomitoci 1,100, wanda kuma ake sa ran zai iya ɗaukar aƙalla ƙafa biliyan Uku, ta iskar gas, a rana guda.
Da ya ke jawabi a ya yin ƙaddamar da Matatar, Shugaban rukunonin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya sha alwashin fara fitar da man da matatar za ta tace zuwa kasuwa, kafin ƙarshen watan Yuli, wanda tuni ma an zarce hakan.