NishaɗiUncategorized

Mawaƙi Rarara Ya Yi Hatsarin Mota

Fitaccen Mawaƙin Siyasa, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu, da aka fi sani da Rarara, ya gamu da hatsarin Mota, a ya yin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Filin Sauka Da Tashin Jiragen Sama.

Mai taimakawa mawaƙin kan Shafukan Sada Zumunta, Rabi’u Garba Gaya, shi ne ya bayyana hakan ta shafinsa na kafar Sadarwar Facebook, da yammacin ranar Juma’a.

Sai dai, ya ce Mawaƙin na cikin ƙoshin lafiya, inda ya yi Addu’ar Allah ya kiyaye aukuwar irin hakan, a nan gaba.

“Mai Girma Shugaban Kasar Mawaka Alhaji Dauda Kahutu Rarara Yayi Hatsarin Mota a Hanyarsa Ta Zuwa Airport, Alhamdulillah Yana Lafiya, Cikin Koshin Lafiya, Allah Ya Kiyaye Gaba Oga.”, a cewar jawabin na Rabi’u Garba Gaya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button