Ƙasashen Ƙetare

Mawaƙin Brazil Ya Mutu Bayan Gizo-Gizo Ya Cije Shi

Mawaƙin ƙasar Brazil, Darlyn Morais, mai shekaru 28 a duniya, ya rasa ransa, bayan ciwon Gizo-Gizo a gidansa, da ke birnin Miranorte, na ƙasar ta Brazil, tun a ranar 31 ga watan Oktoban da ya gabata.

Gizo-Gizon ya ciji Morais ɗin ne a fuskarsa, inda aka garzaya da shi zuwa Asibiti cikin gaggawa, a ranar Lahadi. Ya yin da kuma ya rasu, a ranar Litinin ɗin da ta gabata, 6 ga watan Nuwamban shekarar da mu ke ciki, kamar yadda Jaridar Daily Mail ta rawaito, a ranar Laraba.

Matar mamacin, Jhullyenny Lisboa, ta ce akwai ƴarsa mai shekaru 18 a duniya, wacce itama Gizo-Gizon ya cije ta, aka kuma kwantar da ita a Asibiti, cikin halin Rai-Kwakwai Mutu-Kwakwai.

Lisboa ta ce, sai da launin fuskar mamacin ya sauya, sakamakon cizon, kafin rasuwarsa.

“Ya dinga jin ciwo da kasala a jikinsa ne, kuma fuskarsa ta fara duhu a ranar, 31 ga watan Oktoba. Ya kuma garzaya babban Asibitin Palmas, a ranar ta Lahadi”, a cewarta

Morais dai, ya tsinci kansa a duniyar waƙa ne tun tun ya na da shekaru 15 a duniya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button