Ilimi

Membobinmu Ba Su Shiga Yajin Aiki Ba – Ƙungiyar Malamai Ta CONUA

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta CONUA, ta bayyana cewar membobinta ba su shiga Yajin Aikin SAI BABA TA GANI ɗin da gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC su ka tsunduma a faɗin ƙasar nan ba.

Wani jawabi, mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Niyi Sunmonu, da aka rabawa Manema Labarai, a babban birnin tarayya Abuja, ranar Talata, ya bayyana cewar ƙungiyar ba ta shiga Yajin Aikin ba, saboda ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC ba su tuntuɓeta ba.

Da safiyar ranar Talata ne dai, membobin gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar nan su ka tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani, ciki kuwa har da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU), lamarin da ya jawo tsayawar al’amuran koyo da koyarwa cik! a Jami’o’in ƙasar nan.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button