Messi Bai Sanya Hannu Akan Yarjejeniya Da Al- Hilal Ba – Mahaifinsa
Jorge Messi wanda ke zama Mahaifi ga dan wasa Lionel Messi ya musanta jita-jitar da ake yadawa kan rantaba hannun dansa akan yarjejeniya da kungiyar Al Hilal ta kasar Saudi Arabia Kawo karshen zangon wasannin dan wasan na gaba dai, ana ganin yakan iya zama silar komawarsa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona. Ko kuma ya tsallaka kasar ta Saudia domin samun kungiyar da zai dinga karbar manyan kudade.
Bayan da ake tsammanin cigaba da kasancewarsa a kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-German abu ne mai matukar wahala.
Ana ganin burikan dan wasan sun karu ne dai, bayan da ya lashewa kasarsa ta Argentina kofinm duniya, wanda hakan ya sanya masa azamar ganin ya sake sanya mata riga a wasan kofin duniyar karo na gaba.
Wata kafar yada labaran Faransa dai, ta rawaito cewar dan wasan Messi na gudanar da tattaunawar baka da baka da wata kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya da ba a kai ga bayyana sunanta ba, wanda ake ganin yunkurin a matsayin wani abu da ka iya sake hada shi inuwa guda da takwaransa Christiano Ronaldo.
A yanzu dai, dukkannin kungiyoyin kwallon kafa na Barcelona da Al Hilal su na fatan ganin sun sake mallakar dan wasan Messi, wanda zai cika shekaru 36 a wata mai kamawa, wanda kuma ya ke c igaba da nuna shaáwar bugawa tawagarsa ta Argentina wasa.