Minista Ya Fusata, Bayan Rasa Ko Da Kocin Najeriya Ɗaya, A Jerin Alƙalan Wasannin Kofin Afirka
Rasa ko da guda daga cikin Alƙalan wasannin Najeriya, a jerin Alƙalan wasannin da za su yi busa a ya yin buga gasar kofin ƙasashen Afirka, da za ta gudana a watan Janairun 2024 a ƙasar Cote D’Ivoire, ya fusata Ministan Wasannin Najeriya, John Owan Enoh.
John Enoh, ya bayyana rashin jindaɗinsa ne, ranar Alhamis, a babban birnin tarayya Abuja, kan jerin Alƙalan wasannin da CAF ta fitar, da za su jagoranci wasan da ake shirin fara wa a watan Janairu.
Inda ya ce, idan aka yi duba da ƙarfin da tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ke da shi, da ma tarin mutanen da ƙasar ta mallaka, to tabbas bai kamata ace Najeriyar ta tsinci kanta a wannan hali, wanda ke cigaba da ɗaukar hankalin duniya ba.
Ministan, ya sha alwashin tattauna da dukkannin masu ruwa da tsaki, da su ka haɗar da hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (NFF), da ƙungiyar Alƙalan Wasa ta ƙasa (NRA), da makamantansu, dan ganin an lalubo hanyar da za a ɓullowa wannan batu.
“A gasar kofin ƙasashen Afirka ta ƙasar da aka gudanar (2021), Najeriya Mataimakin Alƙalin Wasa ɗaya kawai ta samu, a jerin dukkannin masu ruwa da tsakin gasar. Yanzu kuma bayan shekaru biyu, ba mu da wakili ko ɗaya ma.
“Har kawo gasar AFCON ta gaba (2023) kumamawa bamu da ko da mutum guda, a jerin masu ruwa da tsaki. Dole na kawo ƙarshen wannan lamarin.
“Za mu tattauna da NFF, ƙungiyar Alƙalan wasanni, da ma hukumar da ke shirya gasar, saboda muna buƙatar gano daga ina wannan matsalar ta samo asali”, a cewarsa.
A ƙarshe, ya kuma bayyana irin ƙoƙarin da ya ke yi, wajen magance matsalolin da ɓangaren wasanni ke fuskanta, a ƙasar nan.