Ilimi

Ministan Ilimi Ya Gabatar Da Sabuwar Manhajar Karatun Jami’o’i Ga NUC

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya gabatar da sabuwar manhajar karatun Jamióín kasar nan, ya na mai cewar manhajar zata tallafa matuka wajen karawa Daliban da su ka kammala karatu a Jamióín cikin gida kima.

Adamu, ya bayyana hakan ne, a ya yin taron gabatarwa da alúmma sabuwar manhajar, da Jamióí, kashi na farko, da aka gudanar, ranar Talata, a babban birnin tarayya Abuja. Ya na mai cewar, sabuwar manhajar karatun zata tallafa wajen samarwa dalibai dukkannin kwarewar da su ke da bukata, Ilimi, da ma gogayyar karni na 21.

Adamu, ya kuma yi kira da a kaddamar da manhajar, inda ya ce za a bayyanar da ita ga sassa 17 ciki kuwa har da hukumar kula da Jamióí ta kasa NUC, dan tabbatar da cewar kasar nan ta taka matakin cigaban duniya.

Inda Ministan ya ce koma bayan da ake fuskanta ta fuskar Ilimi a halin yanzu, musamman ma a yankin Arewa mutanen yankin ne sanadiyyar aukuwar hakan.

Adamu ya kuma bayyana farincikinsa game da lasisin da Gwamnatin tarayya ta bawa sababbin Jamioí masu zaman kansu kimanin 37, a ranar Litinin, ya yin da kuma mafi yawa daga cikinsu za su kasance ne a yankin Arewa.

Ya kuma yi kira da a samar da hukumar kula da alámuran Malamai, ya na mai cewar, yunkurin abu ne da zai haifar da kyakykyawan sakamako a fannin koyarwa. A nasa jawabin, Babban Sakataren hukumar kula da Jamióí ta kasa NUC, Farfesa Rasheed Abubakar yabawa ministan ya yi kan tarin ire-iren cigaban da ya samar wajen bunkasa Jamióín kasar nan.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button