Ilimi

Muhimmiyar Sanarwa Ga Ɗaliban Jami’ar Bayero

Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero, da ke birnin Kano, ta fitar da sanarwar komawa domin cigaba da rubuta jarrabawar ƙarshen zangon karatu na farko (First Semester), na kakar karatu ta 2022/2023, biyo bayan janye Yajin Aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC su ka yi, da yammacin jiya (Laraba).

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Magatakardar Jami’ar, Amina Umar Abdullahi, ta bayyana cewar, taron da Kwamitin zartarwa na Jami’ar ya gudanar, a yau, ya amince da gobe (Juma’a), 17 ga watan Nuwamba, a matsayin ranar da Ɗaliban da ke karatun Digirin farko a Jami’ar za su cigaba da rubuta jarrabawoyinsu, bayan da aka koma Makaranta a yau (Alhamis) 16 ga watan Nuwamban 2023.

Ka zalika, sanarwar ta ce, dukkannin jarrabawoyin da aka tsara rubutawa a ranaku biyun da aka fuskanci Yajin Aiki, wato Talata da Laraba 14 da 15 ga watan Nuwamba, a yanzu za a rubuta su ne, bayan kammala jarrabawar ranar ƙarshe.

Ka zalika, sanarwar ta buƙaci ɗaliban da su saurari sanarwa game da jarrabawoyin waɗanda ba a rubuta ba, daga tsangayoyinsu.

Idan ba a manta ba dai, a ranar Talatar da ta gabata ne, Jami’ar Bayero ta fitar da sanarwar ɗage cigaba da rubuta jarrabawoyin da ta ke yi, har sai abin da hali ya yi, sakamakon matakin da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar ta ɗauka, na yin biyayya ga uwar ƙungiyar ƙwadago, wacce ta umarci a tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button