Zamantakewa

Mun Bawa Fasiƙan Da Ke Son Tuba Wa’adin Makonni Biyu – Sheikh Daurawa

Babban Kwamandan rundunar nan da ke umarni da kyawawan ayyuka, tare da hani da munana (HISBAH) ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bada wa’adin makonni biyu ga Fasiƙai, Karuwai, har ma da Ƴan Daudun da ke son tuba, tare da gyara halayensu, da su halarci ofishin hukumar, domin karɓar nasihohi, tare da form ɗin jari.

Daurawa, ya bayyana hakan ne, a daren Litinin, ya yin da ya ke zantawa da sashen Hausa na BBC, kan sakamakon tattaunawar sulhun da su ka yi da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da komawarsa kujerar shugabancin hukumar ta HISBAH, bayan bayyana ajiye muƙamin da ya yi, a ƙarshen makon da ya gabata.

A tattaunawar tasu kuma, Daurawa ya ce Gwamnan ya yi alƙawarin samarwa da hukumar ƙarin kayayyakin aiki, domin bunƙasa ayyukanta.

Ka zalika, ya ce za a samar da makaranta ta musamman mai suna ‘Hisbah Training School’ da za ta dinga horas da Jami’an hukumar, ba ya ga sashen fasahar zamani da za a samar, haɗi da sashen kula da al’amuran shari’a.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button