Ilimi

Mun Kai Gaɓar Da Mu Ke Satar Kayan Abinci Mu Gudu – Ɗaliban Najeriya, A Iyakar Egypt

Ɗaliban ƙasar nan, da su ka dawo Najeriya cikin daren jiya (Laraba), daga Egypt, sun bayyana yadda rayuwarsu ta kasance kafin samun damar dawowa gida, inda su ka ce wasu daga cikin matan da ke tare da su an ci zarafinsu ta fuskar fyaɗe, sakamakon mummunan yanayin da su ka tsinci kansu, wanda har ya kai ga su na zuwa shaguna su saci kaya, su tsere.

Wata ɗaliba mace, daga cikin ɗaliban da su ka dawo, a ya yin saukarsu a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa da ke Abuja, ta bayyana wa ƴan Jaridu yadda ake cin zarafin su, tare da marinsu da ake yi a cikin jama’a.

”Mun kashe dukkannin kuɗin da mu ke da shi. Su na cin zarafinmu ta hanyar yi mana fyaɗe. Babu abinci, babu ruwan sha. Sai da ta kai lokacin da mu ke zuwa shaguna mu saci abubuwa mu gudu ma”, cewar matashiyar ɗalibar, a ya yin da su ke kan iyaka.

Ita ma wata ɗalibar ta daban, ta bayyana wa Sashen Hausa na BBC a ya yin zantawarta da su cewar, ƙafofinsu sun ƙame, saboda dogon lokacin da su ka shafe a Motoci.

A nasa ɓangaren, shi kuwa wani ɗalibi namiji ya ce, yanayin ya yi matuƙar muni, domin kuwa har biyan kuɗi su ke kafin a barsu su yi fitsari, inda ya kuma yi fatan kawo ƙarshen wannan yaƙi cikin ƙanƙanin lokaci, domin samun damar komawa Sudan, dan kammala zangon karatunsa na ƙarshe.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button