Muna Yin Bakin Ƙoƙarinmu Wajen Ganin Mun Buɗe Jami’ar Sufuri – Shugaba Buhari
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewar gwamnatin sa na iya ƙoƙarinta wajen ganin ta buɗe Jami’ar sufuri a garin Daura, da ke jihar Katsina, wacce kuma za ta kasance irinta ta farko a ƙasar nan.
Buhari, ya kuma ƙara da cewar, ƙudirin buɗe Jami’ar, zai taimaka matuƙa, wajen tallafar ƙoƙarin gwamnatinsa na samar da haziƙan Ɗalibai, a fannoni mabanbanta, da su ka shafi sufuri, musamman ma sufurin jirgin ƙasa, wanda abu da zai bunƙasa walwalar ƴan ƙasa da ma cigaban tattalin arziƙi.
Shugaban ya bayyana hakan ne a jihar Legas ya yin ƙaddamar da ƙananan jiragen ƙasa a Kajola, da ke jihar Ogun, wacce ta kasance ɗaya tilo a faɗin yammacin Afirika , da ke da wadatattun jiragen zamani .
Shugaban wanda ya samu wakilcin Ministan sufuri, Mu’azu Sambo ya ƙara da cewar : ana sa ran samar da ɗalibai daga Jami’ar ta sufuri da ke daura, da ma waɗanda ake sa ran dawowar su daga mabanbantan jami’o’in da ke ƙasar China, waɗanda su ka samu tallafin karatu, za su cike guraben Aikin da ake da su, a kamfanin sufurin jiragen ƙasan na Kajola Assembly Plant.