Labarai

Mutane 5 Sun Mutu Yayin Haɗarin Jirgin Ruwa, A Kano

Hkumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar mutuwar mutane biyar, ya yin da shida suka tsira da raunuka, a wani hatsarin jirgin ruwa, da aka yi, a madatsar ruwa ta Kanwa, da ke ƙaramar hukumar Madobi ta jihar Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa, cikin tattaunawar da su ka yi ta wayar tarho cewar, wani mutum mai suna, Umar Faruk-Dalada ne ya sanar da su aukuwar lamarin.

Ya kuma tabbatar da cewar, hatsarin ya faru ne a jiya Lahadi, 22 ga watan Afirilu, da misalin 5:40 na yamma.

Bayan hatsarin Jirgin mai ɗauke da mutun 11 dai, an samu damar tseratar da mutane 6 a raye, ya yin da 5 daga ciki kuwa su ka tsira a yanayin na buƙatar agajin gaggawa.

Kakakin ya kuma ƙara da bayyana sunayen waɗanda su ka rasa rayukan su, da su ka haɗar da : Abdulrazak Nabara, mai shekaru 40; sai Ɗalha Muktar-Atamma, da shima ke da shekaru 40; Mustapha Ibrahim, mai 45; Umar Isah, mai shekaru 35, da Umar Idris, mai shekaru 35, a duniya.

Jami’in ya ƙara da cewar, waɗanda hatsarin ya ritsa da su sun fito ne daga unguwar Fagge, da ke ƙaramar hukumar Faggen a jihar Kano.

Kuma tuni aka ƙaddamar da binkice domin gano sanadiyyar kifewar jirgin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button