Mutanen Da Su Ka Amfana Da Bashin COVID-19 Sun Koka, Bayan Da CBN Ya Buƙaci Su Biya
Babban bankin ƙasa CBN ya shirya tsaf! domin karɓar biyan basussukan COVID-19 da ya bayar ga wasu daga cikin al’ummar Najeriya, da nufin shawo kan matsin tattalin arziƙin da aka fuskanta a wancan lokacin.
Kamfanin dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewar, bankin ya bayar da basussukan ne ta tsarin TCF, ga wasu daga cikin jama’ar Najeriya, a shekarar 2020, da nufin rage wa al’umma raɗaɗin rusa tattalin arziƙin da annobar COVID-19 ta haifar musu.
Wasu daga cikin waɗanda su ka amfana da basussukan dai, sun bayyana damuwarsu kan salon da bankin ya ɗauka wajen karɓar kuɗaɗensa.
Inda guda daga cikinsu mai suna, Fatimah Alli, ta bayyana cewar, yunƙurin cire biyan bashin 500,000 ɗin da bankin ya ke binta, ta rancen COVID-19 da ta amfana da shi ya haifar mata da gagaruman ƙalubale a tattalin arziƙinta.
“Na samu rancen Naira 500,000 a shekarar 2020, domin rage raɗaɗin matsin tattalin arziƙin da COVID-19 ta jefa al’umma. Amma a wancan lokacin mun yi imanin cewar ba za mu biya kuɗaɗen ba.
“Amma a ƴan kwanakin nan, sai CBN ya cire dukkannin kuɗin da su ke bankina, a matsayin wani sashe na biyan bashin rancen”, a cewarta.
Shi ma wani wanda ya amfana da bashin na TCF, Abbas Sule, kokawa ya yi da yadda ake cire kuɗaɗen biyan bashin daga Asusun bankinsa.
“Lokacin da na samu rancen a shekarar 2020, Ma’aikacin bankin NIRSAL da ya tsaya min wajen fitowar kuɗin ya karɓi Naira 50,000, inda aka bani 450,000.
“Amma yanzu, su na son na biya 500,000, kuma hakan ba Adalci bane”, a cewarsa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito yadda bankin NIRSAL a ƴan kwanakin nan ya sake kira ga Magidanta, da ma mamallakan kasuwanci a ƙasar nan, da su biya kuɗaɗen rancen na COVID-19 da su ka amfana da shi.
A watan Maris ɗin shekarar 2020 ne dai, Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya ɓullo da tsarin rabon Naira biliyan 50 a tsarin TCF a matsayin rance, ga Magidanta da Masu ƙananan Sana’o’i, sakamakon illar da annobar COVID-19 ta haifar ga kasuwanci.