Mutuncin Daurawa Ya Dame Gwamnatin Kano Ya Shanye – Sani Zangina
Tauraron ɗan siyasar nan, wanda ya yi shura a fannin sharhi kan al’amuran yau da kullum, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya bayyana cewar, mutuncin tsohon Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya dame na gwamnatin Kano ya shanye, za kuma ta iya rasa dukkannin wata kara da take samu, sakamakon fushin Shehin Malamin.
Alhaji Zangina, ya bayyana hakan ne, ranar Juma’ar da ta gabata, ta shafinsa na Facebook, Jim kaɗan bayan Malamin ya bayyana ajiye muƙaminsa na shugabancin hukumar HISBAH ta jihar Kano, sakamakon wasu kalaman suka ga hukumar da ya ce Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi, wanda kuma hakan abune da ya sace masa ƙwarin guiwar da ya ke da shi.
“Ya kamata Gwamnatin Kano tasan cewa mutuncin Daurawa ya dameta ya shanye, kuma duk wata kaara da take samu zata iya rasa shi da fushin Sheikh Daurawa.
“Daurawa yafi mana gwamnatin kano da abinda ke cikinta.”, a cewarsa.
Kafin hakan kuma, Alhaji Zanginan ya buƙaci Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya fito ya janye kalamansa, ya yin da a gefe guda ya yi kira ga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya koma kan muƙaminsa.
Ya na mai cewa, “Akwai bukatar Gwamnan Kano ya fito ya janye kalamansa shi kuma sheikh Daurawa ya koma mukaminsa.”