Na Baka Kwana Uku Ka Janye Barazanar Da Ka Yi Wa Amdaz – Martanin Alhaji Sani Ga Darakta Sheshe
Fitaccen Ɗan Gwagwarmayar nan, kuma Ɗan Jarida, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a akan Daraktan Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Alhaji Sheshe, muddin ya gaza janye barazanar da ya yi wa, Jarumi Abdallah Amdaz, cikin sa’o’i 72.
Alhaji Sani Zangina, ya bada wannan wa’adi na tsawon kwanaki uku ne, ta shafinsa na kafar sada zumunta ta Facebook, da yammacin ranar Alhamis.
Wa’adin kwanaki ukun da Fitaccen Ɗan Jaridar ya bayar dai, zai kawo ƙarshe ne, a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamban da mu ke ciki.
“Zan dauki matakin Shari’ah ta gaskiya akanka matukar baka janye barazanar ka akan Amdaz ba.
“Darakta Sheshe da fatan sakon zai iskeka.
“Kanada kwana Uku zuwa Litinin 20th Nov. 2023.”, a cewarsa.
Fitaccen Daraktan, ta hannun Lauyoyinsa: Barista Nnamdi Onana; Barista Nkiru Joseph; da Barista M. I. Baba, ya aike da wata wasiƙa ga Jarumin, ya na buƙatarsa da ya fito cikin jama’a ya bawa ɗaukacin ƴan masana’antar ta Kannywood haƙuri, bisa zargin ɓata musu sunan da ya yi, cikin awanni 48, ko kuma ya maka shi ƙara a gaban Kotu.
Abdallah Amdaz, ya fara fuskantar suka da tarin ƙalubale daga ƴan Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ne dai, tun bayan wasu kalamai da ya furta, a ya yin da ya halarci helikwatar hukumar Hisbah ta jihar Kano, domin amsa gayyatar da ta yi musu, a ranar Litinin ɗin da ta gabata, inda da dama daga ciki su ka ƙuduri aniyar daina saka shi a cikin fina-finansu, ya yin da wasu kuwa ke barazanar shigar da shi ƙara a gaban Kotu.
Daga cikin kalaman da Jarumin ya furta waɗanda ƴan masana’antar ke wa kallon cin zarafi da ɓata suna, akwai bayyana dalilai uku waɗanda ya ce su ne dalilan da ke sanya jama’a shiga harkar film, da su ka haɗar da: Karuwanci; Kawalci; da ma neman ɗaukaka.
Inda ya jaddada buƙatar da ke akwai, ta tsaftace masana’antar, duba da tarin ɓarnar da ke cikinta.