Nishaɗi

Na Janye Kalamaina Kan Mawaƙan Arewa – Sani Ahmad

Fitaccen Ɗan Siyasa, Ɗan Kasuwa, kuma mai riƙe da Sarautar Gargajiya, Alhaji Sani Ahmad Zangina ya sanar da janye kalaman da ya furta akan Mawaƙan Arewa, a ya yin wata hirar rabin sa’a da ya gudanar, a tashar DCL Hausa.

Alhaji Sani, ya sanar da janye kalaman nasa ne, ta cikin wani saƙon rubutu da ya wallafa, a shafinsa na Facebook, a daren ranar Juma’a.

Inda ya bayyana cewar, ya amince da janye kalaman nasa a kan Mawaƙan ne, bayan barranta kansu da su ka yi, da kalaman da Fitaccen Mawaƙin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara ya furta, akan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Sai dai, ya buƙaci gamayyar Mawaƙan da su haɗa hannu domin hukunta Rararan, wanda ke neman zamewa ‘waƙe ɗaya ɓata gari’, a cikinsu.

Ga dai saƙon, kamar haka: “Na janye kalamaina kan mawakan arewa da nayiwa jam’u bayan sun barranta kansu da kalaman Rarara akan Baba Buhari.

“Ya dace dai su hukuntashi inda hali…”, a cewarsa.

Idan za a iya tunawa dai, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya caccaki gamayyar Mawaƙan na Arewa, tare da kiransu da ‘Maroƙa’, ta hanyar buga misalin cewa babu wanda za a bawa kuɗi a cikinsu, kafin, ko bayan rera waƙa, ya ƙi karɓa.

Iƙirarin na Alhaji Sani kuma, na a matsayin martani ne kan kalaman da Mawaƙin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu ya furta, akan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bayan da ya zarge shi da damalmala ƙasar, kafin miƙata ga sabon shugaban ƙasa na yanzu, Alhaji Bola Ahmed Tinubu.

Sai dai, wasu daga cikin fitattun Mawaƙa irin su, Ali Jita, El-Mu’az Kaduna, Ado Gwanja da Baban Chinedu, sun fito sun barranta kansu da kalaman mawaƙin, waɗanda ke matuƙar kamanceceniya da butulcewa tsohon shugaban ƙasar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button