Na Kare Ƴancin Ƴan Jaridu, A Zangon Mulkina – Shugaba Buhari
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ce, ya yi matuƙar ƙoƙari wajen kare ƴancin Ƴan Jaridun ƙasar nan, a tsawon shekaru 8 da suka gabata, na zangon mulkinsa.
Shugaban ya bayyana hakane a ranar Talata, ya yin da ya ke tattaunawa da kafafen yaɗa labarai, kan ranar ƴancin Ƴan Jaridu ta duniya, mai taken Inganta damarmakin gobe: ta hanyar amfani da ƴancin yaɗa labarai, a matsayin jagaba, wajen ƙwato sauran damarmaki.
A Bikin na bana, wanda ke cika shekaru 30, tun bayan da majalisar ɗinkin duniya, ta ayyana samar da wata rana ta ƴancin yaɗa labarai, Buhari ya ce ana amfani da shi wajen tunawa da zaratan Ƴan Jaridar da su ka fuskanci haɗurran rasa rayukansu a fafutukarsu ta Ilimantar da al’umma, da ma faɗakar da su.
Ya kuma buƙaci manema labarai, da su cigaba da kasancewa masu sadaukar da kai, da yin aiki dan cigaban ƙasa, da ma amfanar ƴancinsu.