Labarai

NAFDAC Ta Haramta Shigo Da Taliyar Indomie

Hukumar kula da abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta haramta shigo da taliyar yara, da aka fi sani da Indomie cikin ƙasar nan.

Wannan mataki na zuwa ne kuma, bayan yawaitar kiraye-kirayen da hukumomin ƙasashen Taiwan, da Malaysia su ka yi, biyo bayan gano sinadarin ‘Ethylene Oxide’ a cikinta, wanda kuma sinadari ne da ke haifar da ciwon daji (Cancer).

Da ta ke fitar da bayanin haramtawar, a ranar Litinin, Darakta Janar ta hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce hukumar za ta fara fitar da samfurin irin taliyar Indomin da ke da wannan illa, a gobe (Talata), wadda kuma ta haɗarda wasu sinadaran ɗanɗano, da taliyar kan zo da su.

Ta kuma ce, za a gudanar da binciken irin wannan taliya, a kasuwanni, tare da bayyana wa al’umma halin da ake ciki, game da ita.

A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO) dai, sinadarin na Ethylene Oxide, sam bashi da launi, kuma ya na da saurin tasiri, a jikin jama’a, ya yin da ya ke ɗauke da siffar iska (gas), wacce ake amfani da ita wajen samar da sinadarai mabanbanta.

WHO, ta kuma ce, a cikin wani binciken sinadarin na Ethylene Oxide da ta gudanar, akan dabbobi, ta gano yadda ya ke taka muhimmiyar rawa wajen haɓɓaka ciwon daji ga bil Adama, a don haka, hukumar ta buƙaci jama’a da su taƙaita amfani da shi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button