Kimiyya Da Fasaha

NAFDAC Ta Samar Da Manhajar Tantance Gurɓatattun Magunguna

Hukumar kula da Abinci ta magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta ƙaddamar da wata Manhaja da ke ƙunshe da bayanan dukkannin halastattun magungunan da ke da rijista.

An kuma sanya wa Manhajar sunan “Greenbook”, za kuma a iya samunta a shafin hukumar.

Babbar Daraktar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ita ce ta bayyana hakan, a ya yin ƙaddamar da Ofishin hukumar na yankin Isolo, da ke jihar Lagos, a ranar Laraba.

A nasa jawabin, Mataimakin Daraktan Sashen Rijista Da Adana Bayanan Intanet na hukumar, Dr. Dunoi Afam, ya ce babbar manufar samar da Manhajar shi ne, bayar da sahihan bayanai kan magungunan da ake shigarwa cikin al’umma.

Shi ma Mataimakin Daraktan Cibiyar Tattara Bayanan Abinci Da Magunguna na hukumar, Khaled Musa ya ce, samar da Manhajar zai sanya ikon gano gurɓatattun magunguna ya karkata zuwa hannun al’umma, tunda kowa ya kan iya mallakar Manhajar daga ɗakinsa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button