Addini

NAHCON TA GARGAƊI MAHAJJATA KAN AMFANI DA GURƁATACCEN ABINCI

Hukumar Aikin Hajji ta kasa NAHCON, ta gargadi Mahajjata kan sayen abinci daga masu abincin da basu samu sahalewarta ba.

A yanzu haka dai, tuni wasu daga cikin maniyyata su ka fara garzayawa kasar Saudi Arabia, domin gudanar da Ibadar ta Aikin Hajji, ta shekarar 2023, wacce guda ce daga cikin shika-shikan Musulunci.

Wakilin hukumar, a birnin Madina, Alhaji Ibrahim Mahmud, shi ne ya yi wannan gargadin ya yin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa, jiya a Madina.

A cewarsa dai, tuni hukumar ta fara sahalewa wasu kwararru a fannin girke-girke, damar samar da abincin da Mahajjatan za su yi amfani da shi, bisa manufar ganin an kare su daga amfani da gurbataccen abinci.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button