Najeriya Da Kuwait Sun Rattaɓa Hannu Kan Yarjejeniyar BASA
Najeriya, da Kuwait sun amince da ƙara ƙarfafa alaƙarsu ta fuskar sufurin jiragen sama, bayan da su ka rattaɓa hannu akan yarjejeniyar BASA.
Wani jawabi da maitaimakawa Ministan sufurin jiragen sama a fannin yaɗa labarai, Tunde Moshood ya fitar, ya bayyana cewar, ƙasashen biyu sun rattaɓa hannu akan yarjejeniyar ne, a ya yin taron ƙasashen duniya kan sauyin yanayi na COP28 da ya ke cigaba da gudana.
Moshood, ya bayyana cewar, bayan amincewar dukkannin ɓangarorin biyu da yarjejeniyar ne, sai aka sanya mata hannu, a ƙasar Saudi Arabia.
Yarjejeniyar kuma, na a matsayin ƙara ƙarfafa alaƙar kasashen biyu na Najeriya da Kuwait ta fuskar hulɗoɗin Demokraɗiyya, aiwatar da dangantaka a buɗe, ƙulla sababbin hulɗoɗi, da ma samun haɗin kai ta fuskar tattalin arziƙi.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya bayyana matuƙar farincikinsa kan amincewa da yarjejeniyar, ya na mai bayyana cewar, za ta taka gagarumar rawa wajen bunƙasa cinikayya, yawon buɗe ido, da ma musayar kasuwanci a tsakanin ɗai-ɗaikun mutanen ƙasashen na Najeriya da Kuwait.