Wasanni

Najeriya Ta Sake Komawa Matsayi Na Biyu, A Wasannin Ƙasashen Afirka

Wasannin kasashen Afirka, karo na 13 da ke cigaba da gudana, na kasancewa cikin yanayin samu da rashi, duk da cewa har yanzu Egypt da ke yankin Arewacin Afirka, na rike da kambunta na kasar da ke kan gaba a wasannin na bana, ya yin da a gefe guda matsayin na biyu a samun tarin kyaututtuka ke tsakanin kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu.

Babban labarin ban shaáwa ga mai sauraro dai, bai wuce yadda a jiya Talata, 19 ga watan Maris din da mu ke ciki, Najeriya ta samu nasarar lashe karin kyaututtuka 7 ba, da su ka hadar da zinare hudu, silver 1, tare da tagulla biyu, inda a yanzu jimillar kyaututtukan da Najeriyar ta mallaka a wasannin na bana su ka kai kimanin 85.

Hakan ne kuma ya sake jaddada mata matsayin kasa ta biyu, ya yin da Afirka ta kudu, ta samu miára koma baya zuwa matsayi na uku.

A yanzu, Najeriya na da jimillar kyaututtukan zinare 31, silver 22, tare da azurfa 32.

Tazarar da ke tsakanin kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu a yanzu bai zarce kyaututtuka uku ba, domin kuwa ita ma Afirka ta kudun na da kyaututtukan zinare 28, silba 29, da azurfa 38, wato jimillar kyaututtuka 94 kenan.

Ita ma Aljeriya da ke a matsayi na hudu, na da kyaututtukan zinare 22, silba 31, har ma da Azurfa 41.

Ita kuwa Tunisia a matsayi na biyar ta tsinci kanta da kyaututtukan zinare 14, silba 21, tare da azurfa 29.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button