Najeriya Za Ta Haɗa Guiwa Da Dubai, Domin Bunƙasa Shirin Ciyar Da Ɗalibai
Gwamnatin tarayya ta tattauna da Jakadan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a Najeriya, Salem Saeed Alshamsi, tare da Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, domin neman agajinsu a fagen shirinta na ciyar da ɗaliban makarantu.
Bayanin hakan na ɗauke ne ta cikin wani jawabi da Babbar Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kan shirin ciyar da Ɗalibai, Dr. Yetunde Adeniji, ta fitar da safiyar yau (Laraba), a babban birnin tarayya Abuja.
Cigaban kuma, na zuwa ne mako guda, bayan da Gwamnatin tarayyar ta sanar da ƙudurinta na ciyar da kimanin ƙananan yara 100,000 da aka raba da muhallansu, a yankin Arewa.
Adeniji, ta bayyana cewar, wakilcinta ya gana da Jakadan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan da Gwamnan ne, a ya yin bikin cikar daular Larabawa shekaru 52, da aka gudanar ranar Litinin a babban birnin tarayya Abuja.
Ta kuma bayyana cewar, dukkannin jakadun guda biyu, sun bayyana shirinsu na bada gudunmawa ɗari-bisa-ɗari, wajen aikin agajin, da gwamnatin tarayyar ta ɗauko.