Ilimi

Nakasa Ba Kasawa ba : Ɗaliba Marar Hannaye Ta Samu Gurbin Karatu A Jami’a

Maryam Umar, matashiyar Ɗaliba ce mai shekaru 22 a duniya, da ke da lalurar rashin hannaye, wacce kuma a yanzu ta samu gurbin karatu, a Jami’ar Jihar Gombe (GSU).

Matashiyar dai, ta samu gurbin karatu ne, domin karantar fannin tattalin arziƙi (ECONOMICS), sai dai kuɗaɗen makaranta, kimanin Naira 81,322 sun tsaya mata.

Da ta ke bayyana buƙatar taimako a ya yin zantawarta da manema labarai, Maryam Umar, ta ce, Iyayenta basu da ƙarfin da za su iya ɗaukar nauyin karatunta.

Inda ta ce, ”Iyayena su na zaune, a BCGA Gombe. Na kammala makarantar Sakandire na a shekarar 2022. Na kuma samu maki 182 a jarrabawar JAMB UTME, kuma ina da Credits huɗu a jarrabawar NECO, da su ka haɗarda Lissafi da Turanci.

”Sai dai, ba ni da kuɗin Registration ɗin da zan biya domin karanta Economics, a jami’ar jihar Gombe. Iyayena basu da kuɗi, hakan ne ya sanya nake buƙatar jama’a su taimaka min, dan kar na rasa damar da na samu”.

Masu sha’awar taimaka mata dai, za su iya sanya abin taimakonsu ta wannan Asusun bankin : 0015749904 – Union Bank – Umar’s.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button