NANS Ta Buƙaci A Dinga Biyan Kowanne Ɗalibi Alawus Ɗin 200,000 A Shekara
Sabon shugaban ƙungiyar Ɗalibai ta ƙasa, Lucky Emonefe, ya buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya amince a dinga bawa ɗalibai alawus ɗin biyan kuɗin Makaranta duk shekara, na Naira 200,000 kowannensu.
A ya yin taron Manema Labarai da ya gudanar, karon farko, ranar Lahadi, a babban birnin tarayya Abuja, Emonefe ya ce, kuɗin zai kasance a matsayin tallafin rage-raɗaɗi ne, duba da halin matsayin tattalin arziƙin da al’ummar ƙasar nan su ka samu kansu, sakamakon matakan da Gwamnatin Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta ke cigaba da ɗauka, na farfaɗo da tattalin arziƙi.
A ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamban da ya gabata ne dai, NANS ɗin ta gudanar da zaɓen sababbin shuwagabanninta.
Ya yin da a ranar Asabar, aka bayyana Emonefe ɗin a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar, cikin tsatstsauran tsaro, inda zai karɓi aiki daga hannun shugaban NANS ɗin mai barin gado, Usman Barambu.