Kotu

NBA Ta Buƙaci Gwamnan Kano Ya Tsige Kwamishina Bisa Barazanar Hallaka Alƙalai

Ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa (NBA) ta yi Allah-Wadai da barazanar hallaka Alƙalan Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar Kano da Kwamishinan ƙasa da safayo na jihar ta Kano, Adamu Aliyu Kibiya ya yi, bayan da ya yi zargin yiwuwar fuskantar rashin adalci a shari’ar da ake fafatawa.

Tun da fari dai, Kwamishinan ya furta kalaman barazanar hallaka Alƙalan ne, ya yin da ya ke jawabi ga magoya bayan jam’iyyar NNPP, ranar Alhamis, ya yin Addu’a ta musamman da aka gudanar, inda ya ce dukkannin Alƙalin da ya karɓi cin hanci domin take gaskiya a ya yin hukunci, to babu shakka zai biya fansar hakan da rayuwarsa.

Faifan bidiyon kalaman nasa, a ya yin zantawarsa da Manema Labarai dai, na cigaba da yamutsa hazo a kafafen sada zumunta na zamani, duba da yadda mai maganar ya kasance ƙusan Gwamnati.

Da ya ke martani kan lamarin, a ranar Juma’a, Shugaban ƙungiyar Lauyoyi ta NBA reshen jihar Kano, Barista Suleiman Gezawa, ya buƙaci Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya sutale Kwamishinan, domin nuna cewar matsayar tasa ba daga Gwamnati ta fito ba.

“An jawo hankalina kan wani labari da guda daga cikin masu ruwa da tsaki a Gwamnatin jihar Kano, ya ke barazanar hallaka Alƙalan da ke sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar Kano, inda ya ke cewa dukkannin wanda daga cikinsu ya karɓi cin hanci, to ya yi shirin biya da rayuwarsa.

“Wannan ba abu ne da za mu lamunta ba, kuma ba zamu bari ya tafi haka sakaka ba. Mu a matsayinmu na ƙungiyar Lauyoyi muna kira ga Gwamna da ya sutale shi, kuma ya nisanta kansa da Gwamnatinsa daga waɗancan kalamai” a cewar Gezawan.

Ka zalika, ya buƙaci Jami’an tsaro da su gudanar da bincike kan lamarin, duba da yadda Kwamishinan ke barazanar kisa cikin ƙwarin gwuiwa.

Shugaban na NBA, ya kuma ce wannan shi ne mataki na farko, kuma akwai matakai na gaba da ƙungiyar za ta ɗauka, muddin aka gaza yin komai kan lamarin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button