Kasuwanci
NCC Ta Dakatar Da Haramtawa GLO Kiran Layukan MTN
Hukumar sadarwa ta ƙasa, NCC, ta dakatar da matakin katse sadarwar kiran waya, tsakanin kamfanin Globacom da MTN Network, zuwa kwanaki 21 masu zuwa.
Hakan na ɗauke ne ta cikin jawabin da Daraktan hulɗa da jama’a na hukumar, Dr. Reuben Muoka, ya fitar, ranar Alhamis, a babban birnin tarayya Abuja.
Mouka, ya ce su na fatan kamfanonin na MTN da GLO za su magance matsalar da ta ɓullo a tsakaninsu, cikin wa’adin na makonni uku.
Kamfanin MTN dai, ya yi yunƙurin dakatar da layukan Glo daga kiran masu amfani da layukansu ne, sakamakon ɗumbin basussukan da ya ke binsa.