NDLEA Ta Kama Masu Shaye-Shaye 85, A Wani Gidan Casu, Da Ke Kano
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta samu nasarar dakume masu shaye-shayen miyagun kwayoyi 85, bayan da ta mamaye wani gidan sharholiya da ke jihar Kano, a daren Litinin.
Bayanin hakan kuma na dauke ne ta cikin wani jawabi, da kwamandan rundunar reshen jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ya fitar, mai dauke da sa hannun kakakin hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari. Inda ya ce, jamián hukumar sun halarci gidan sheke ayar ne, biyo bayan korafe-korafen da aka yi ta fama da su kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, a gidan. Ya kuma ce, mazauna unguwar da gidan ya ke ne su ka kai korafin abubuwan da su ke wakana.
Abubakar Idris Ahmad ya kuma kara da cewar, 55 daga cikin wadanda aka kama din Maza ne, ya yin da 30 su ka kasance Mata, da ma wasu kwayoyi da ake zargin na kasar India ne, wadanda aka samu nasarar kwacewa daga wurinsu.
Kwamandan ya kuma ce, wasu daga cikin wadanda ake zargin sun yi yunkurin tserewa ta hanyar tsallaka katanga, ya yin da wasu kuwa su ka yi kokarin su buya a cikin manyan naúrorin sanyi, amma dukkanninsu Jami’n sun samu nasarar dakume su. Ka zalika, ya kara da cewar, ana tsaka da gudanar da bincike a halin yanzu domin gano dilolin kwaya a cikinsu, kafin gurfanar da su a gaban kuliya.
A karshe, Kwamandan ya yi kira ga jamaá da su kai rahoton dukkannin wasu laifuka da ke da alaka da amfani da miyagun kwayoyi, dama maboyar dilolin kwayoyin da ke jihar nan.