Ilimi

NECO Ba Ta Ƙara Lokacin Rijistar SSCE 2024 Ba

Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun Sakandire ta ƙasa, NECO, ta ce ba ta tsawaita wa’adin rijistar jarrabawar SSCE ta shekarar 2024 ba.

Hukumar ta bayyana hakane, ta cikin wani jawabi da ta fitar, ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, ta hannun Daraktan sashen yaɗa labaranta, Azeez Sani.

Sani, ya ce rijistar wacce aka fara a ranar Litinin, 18 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, za a rufe shi ne a ranar Litinin, 3 ga watan gobe na Yuni.

Sai dai, ya ce akwai damar biyan ƙarin kuɗi na rijista a makare (Late Registration), daga ranar Talata, 4 ga watan Yuni, zuwa Litinin 10 ga watan na Yunin 2024.

Inda ya buƙaci, shuwagabannin makarantu, ma’aikatun Ilimin jihohi, da dukkannin masu ruwa da tsaki, da su yi watsi da rubutun da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na zamani, wanda ke cewa hukumar ta tsawaita wa’adin rijista, zuwa ranar Litinin, 20 ga watan Yuni.

NECO dai, ta tsara fara rubuta jarrabawar SSCE 2024 ne, a ranar 19 ga watan Yuni, yayin da za a kammala a ranar 26 ga watan Yuli.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button