NFF Ta Amince Da Sauya Sunan Gasar Premier Ta Ƙasa
Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (NFF), ta amince da sauya sunan gasar ajin ƙwararru ta ƙasa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), ya rawaito cewar, an tattauna kan batun sauya sunan ne, a ya yin taron da hukumar ta ke gudanarwa na shekara-shekara (AGA) karo na 79, da aka gudanar ranar Lahadi, a Uyo, da ke Jihar Akwa Ibom.
A cewar wata sanarwa da aka fitar, bayan kammala taron dai, NFF ta amince da sauya sunan gasar mai daraja ta ɗaya a ƙasar ne, daga Nigeria Professional Football League (NPFL), zuwa Nigeria Premier Football League (NPL).
Inda sanarwar ta kuma ce, amincewa da sauya sunan, guda ne daga cikin abubuwan da aka amince da su, a ya yin taron.
Idan mai karatu zai iya tunawa dai, a baya, NFF ta bayyanawa hukumar gudanarwar NPL cewar, taron na NFF ne kawai ya ke da ikon sauya wannan suna, ya yin da hukumar gudanarwar NPL ɗin ta ƙaddamar da sabon Logo, da sabon sunan gasar.
Bugu da ƙari, sanarwar ta ce, Shugaban hukumar ta NFF, Ibrahim Gusau, ya kuma godewa taron, bisa yadda su ka amsa buƙatarsa cikin ƙwarin guiwa, da ma membobin kwamitin gudanarwa, a ya yin zaɓukan ƙarshe da su ka gudana.
Ka zalika, ya godewa gwamnatin tarayya, da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa irin goyon bayan da ya ke bayarwa, wajen ganin an cimma muradan wasan ƙwallon ƙafa.