Labarai

Ngige Ya Buƙaci Gwamnatin Tinubu Ta Sake Duba Mafi Ƙarancin Albashi

Ministan ƙwadago, da nagartar Aiki, Chris Ngige, ya bayyana cewar, Gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, za ta sake duba akan mas’alar mafi ƙarancin albashi, da ke kan Naira 30,000 yanzu haka, a Najeriya.

Ngige dai, ya kasance memba a kwamitin da ya yi aikin duba kan mafi ƙarancin albashi, a shekarar 2019, inda aka sauya adadin mafi ƙarancin albashin daga Naira 18,000 zuwa 30,000, kamar yadda ya ke a dokance kuma, ana duba kan mafi ƙarancin albashin ne, a dukkannin bayan shekaru biyar, dan ganin buƙar ƙara shi, ko akasin haka.

Ministan, wanda ya bayyana haka, a ya yin zantawarsa da tashar Talabijin ta Channels, a cikin shirin siyasa na ‘Politics Today’, na ranar Laraba, ya ce batun sake duba mafi ƙarancin albashin zai kasance daga cikin bayanan da zai miƙa da zarar an rantsar da sabuwar Gwamnati, a cikin watan Mayun da ke tafe, gabanin aiwatar da shi, da a cewar sa zai iya kaiwa 2024.

Ngige ya kuma ce, ɓangarorin da lamarin zai shafa sun haɗar da na Gwamnati, masu zaman kansu, da ma na Gwamnatocin jihohi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button