Kasuwanci

NNPC Ya Cigaba Da Haƙar Man Fetur, A Borno

Kamfanin mai na ƙasa NNPC, ya cigaba da gangamin tonon mai, a Wadi-B, da ke ƙaramar hukumar Jere, ta jihar Borno.

NNPC, ya dawo cigaba da haƙan man a Wadi-B ne dai, bayan dakatarwar da ya yi a shekarar 1995, sakamakon ƙalubalen rashin nasarar da aka fuskanta, bayan samun rauni, da koma bayan kasuwanci, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A cewar Shugaban kamfanin na NNPC, Mele Kyari dai, kamfanin na yin iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya tsame mutane daga halin fatara, ta hanyar ɗaukar matakan bunƙasa samar da mai, dan zama jagorar nahiyar Afirka, ta fuskar tattalin Arziƙi.

Kyari ya kuma bayyana hakan ne, a ya yin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke ƙaddamar da gangamin cigaba da haƙan man, a yankin na Wadi-B, da ke jihar Borno.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button