NNPP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Zaɓen Kano, Tare Da Shan Alwashin Ɗaukaka Ƙara
Jam’iyyar NNPP ta yi watsi da hukuncin da Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar Kano, ta zartar a yau, inda tace hukuncin wanda ya sutale Gwamnanta, Abba Kabir Yusuf, abin dariya ne.
Ta cikin wani jawabi da ya fitar, Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Kawu Ali, ya ce jam’iyyarsu ta samu labarin, sai dai ta gaza aminta da yadda Kotun sauraron ƙarar zaɓen ta yanke wannan hukunci, wanda kwata-kwata babu Adalci a cikinsa.
Inda ya ce jam’iyyar ta NNPP za ta ɗaukaka ƙara, kuma tana roƙon magoya bayanta da su cigaba da haƙuri, domin wannan hukuncin ba Mai tabbata bane.
A ya yin tattaunawar AIT da Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na riƙon ƙwarya, Oladipo Johnson, ya ce, zuwa yanzu jam’iyyar bata karanta ƙunshin hukuncin ba, amma tabbatas Kotun ba ta da wani hurumi na sutale Gwamnan jam’iyyar tasu.
Da yammacin Laraba ne dai, Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar Kano, ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna, na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan jihar, bayan da ta soke wasu ƙuri’u kimanin 165,633 da tace an yi aringizonsu.