Siyasa

NNPP Za Ta Shekara 50 Bata Taɓa Ƙasa Ba, Muddin Za a Dinga Amfani Da Shawarar Kwankwaso – Alhaji Sani

Shahararren Mai Sharshin nan kan al’amuran yau da kullum, musammanma ta fuskar siyasa, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya yi hasashen yiwuwar Gwamnatin NNPP ta shafe shekaru hamsin bata faɗi zaɓe ba a jihar Kano, muddin Gwamna Abba Kabir Yusuf zai cigaba da amfani da shawarwarin da Jagoran ɗarikar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ke bawa gwamnatin.

Sani Zangina, ya wallafa wannan hasashe nasa ne, da yammacin Lahadi, ta shafinsa na Facebook.

Yana mai cewar, “Madamar Jagora mai girma kwankwaso zai rika bada shawara kuma gwamnatin Abba tana amfani da shawarar to gwamnatin NNPP tana iya shekaru 50 bata taba kasa ba.”, a cewarsa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button