Wasanni
NPFL: Kano Pillars Ta Lallasa Gombe United Da Ci 2 – 5
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ta lallasa takwararta ta Gombe United, a wasan da su ka fafata da yammacin yau, a cigaba da gasar Premier ta ƙasa.
Kano Pillars ta zura dukkannin ƙwallaye 5 ɗinne ta hannun ɗan wasanta mai suna, Yusuf Abdullahi, a mintinuna na 7, na 14, na 33, na 35, na 45, sai kuma ƙwallo ta ƙarshe da ya zura a mintuna goman ƙarshe.
An kuma samu tsaiko a filin fafata wasan bayan shafe sama da mintuna 30 da farawa, inda magoya baya su ka cika tsakiyar filin wasan, da ke Pantami, a jihar Gombe.
Kafin fafata wasan na yau kuma, Kano Pillars na a matsayin ta 13 ne a teburin gasar ta Premier, ya yin da Gombe United ta ke a matsayin ta 16 a gasar.