NPFL Ta Rabauta Da Dalar Amurka Miliyan 5, Domin Haska Wasannin Kaitsaye
Kwamitin da ke da Alhakin shirya gasar ajin ƙwararru ta ƙasa, haɗin guiwa da GTI, da ma Hukumar bunƙasa wasanni a nahiyar Afirka, sun samu tagomashin maƙudan kuɗaɗe kimanin Dalar Amurka Miliyan 5, da aka damƙa musu domin yin amfani da ita wajen haska wasannin da za a gudanar, ta kafafen sadarwa na zamani, a kakar wasanni ta 2023 zuwa 2024.
A ranar Talata ne dai, sashen da ke da alhakin shirya gasar ajin ƙwararrun ta ƙasa NPFL, ya bayyana cewar gasar zata kasance ta farko a nahiyar Afirka, da za a yi amfani da fasahar Artificial Intelligence, a ya yin gudanar da ita.
Ana kuma sa ran za a dinga haska wasannin ne ta manhajar NPFL Live, wacce manhaja ce da zata bada damar nuna wasannin kaitsaye a lokutan da ake gudanar da su, tare da bawa magoya baya damar more sassauƙan tsarin da manhajar ke da shi kan shaánonin wasannin gida, dama na ƙasashen ƙetare.