Ilimi

NUC Ta Buƙaci Likitoci Su Shiga Aikin Koyarwa

Kwamitin da aka ɗorawa alhakin binciko halin da Ilimin lafiya ke ciki a Jami’o’in ƙasar nan, ya samu zarafin tattaunawa da babban Sakataren hukumar kula da Jami’o’I ta ƙasa (NUC), Farfesa Abubakar Rasheed, domin gabatar masa da daftarin rahoton aikin da aka kallafa musu.

Hakan kuma na zuwa ne, a dai-dai lokacin da hukumar ta NUC ke cigaba da bayyana matsayarta na buƙatar ƙwararrun Likitoci a fannin koyarwa, domin ƙyanƙyashe ƙwararrun Likitoci, masu Karatun Digiri na Biyu, da na Uku, da ma samun Farfesoshi, a fagen.

Jaridar PUNCH dai, ta rawaito yadda ake cigaba da samun sa toka sa katsi kan buƙatar shigar da manyan likitocin fagen bunƙasa Iliminsu, zuwa Digiri na biyu wato Masters, da Digirin Digir-gir wato Doctorate.

Tun da farko dai, babban Sakataren hukumar ta NUC ne ya ƙaddamar da tsarin na Digirin Digirgir a fannin Likitan Fiɗa, saboda dalilai da dama da ya bayyana, waɗanda ke da alaƙa da shirin bunƙasa fannin na Likitancin fiɗa, duba da yadda masu tasowa a fagen ke gaza maye gurbin magabata.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button