Siyasa

PDP Ta Lashe Zaɓe A Dukkannin Ƙananan Hukumomin Oyo

Jam’iyyar PDP, mai alamar lema, ta lashe zaɓen ciyamomi, a dukkannin ƙananan hukumomin jihar Oyo guda 33.

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (OYSIEC), Isiaka Olagunju, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen na ranar Asabar ɗin da ta gabata, a yayin taron manema labarai da aka gudanar, a helikwatar hukumar da ke Ibadan, a yau (Lahadi).

Olagunju, ya kuma alaƙanta wannan gagarumar nasara da PDP ɗin ta samu a jihar, da irin gudunmawar da Gwamna Seyi Makinde, da sauran masu ruwa da tsaki, suke bayarwa ga jihar.

Shugaban na OYSIEC, wanda kuma shi ne Jami’i mai sanar da sakamako, ya ƙara da bayyana wasu ɓangarorin zaɓen, da suke buƙatar a ƙara bunƙasa su.

Inda ya ce, ɓangarorin za su bayyana a rahoton zaɓen, da za a miƙa wa gwamnatin jihar.

Ka zalika, ya kuma yabawa wakilan jam’iyyu, bisa irin gudunmawa da haɗin kan da suka bawa hukumar, wajen ganin an gudanar da sahihin zaɓe.

A nasa ɓangaren, Gwamna Seyi Makinde, ya yaba kan irin kyakykyawan tsaron da aka samu a zaɓen na ranar Asabar, ya na mai cewar, ba a fuskanci wani hargitsi, ko tashin hankali a yayin zaɓen ba.

A nasa jawabin na daban, zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar, Ibadan ta Arewa Maso Gabas, wanda ya sake ɗarewa kujerarsa, Ibrahim Akintayo, ya sha alwashin kyautatawa al’ummar ƙaramar hukumar tasa, fiye da irin abin da suka gani a baya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button