Siyasa

Peter Obi Ya Kaiwa Atiku Ziyara A Karon Farko, Tun Bayan Zaɓen 2023

Jagoran jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya kaiwa tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP, a zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar ziyara, a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Atiku, shi ne ya bayyana ziyarar da Peter Obi ɗin ya kai masa, ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta ta X.

Inda Atiku ɗin ke cewa, “Na yi matuƙar farincikin karɓar baƙuncin #PeterObi a yau”, cikin harshen Ingilishi.

A gefe guda kuma, Peter Obi ɗin, ya kai ziyara ga tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a gidansa da ke Abuja.

Sai dai, har ya zuwa yanzu babu wani bayani da ke bayyana batutuwan da Peter Obi ɗin ya tattauna da shuwagabannin da ya kaiwa ziyara.

Amma, ana ganin ba ya rasa nasaba da miƙa buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe a tsakaninsu, wajen kawar da Gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a zaɓen shekarar 2027.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button