Qatar Ta Ƙauracewa Tattaunawar Kasuwanci Da Najeriya
Gwamnatin Qatar, ta yi fatali da buƙatar Najeriya ta gudanar da tattaunawar zauren sanya hannayen jari (BIF), ya yin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke shirin kai ziyara ƙasar, a farkon watan Maris.
Wata wasiƙa da ƙaramin Ofishin Jakadancin Qatar da ke babban birnin tarayya Abuja ya fitar, tare da aiketa ga Ma’aikatar harkokin ƙasashen wajen Najeriya, mai ɗauke da kwanan watan 22 ga watan Fabrairun 2024 ta bayyana cewar, Qatar ɗin bata Ƙulla wata yarjejeniyar Kasuwanci da Najeriya ba.
Bugu da ƙari, wasiƙar ta kuma ƙara da cewar, Ministan Kasuwancin ƙasar ta Qatar zai fita domin gudanar da aiki na musamman a wajen ƙasar, ya yin ziyarar shugaba Tinubu a ƙasar.
A nata ɓangaren, Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce babu gudu ba ja da baya kan ziyarar shugaban ƙasar Najeriyar zuwa Qatar, a watan Maris, kamar yadda aka tsara.
Tinubu zai kai ziyarar ne dai, a ranakun 2 da 3 ga watan Maris mai kamawa.