Labarai

Raba Motocin Alfarma Ga Ƴan Majalissar Dokokin Kebbi, Na Cigaba Da Yamutsa Hazo

Al’umma da dama, na cigaba da tofa albarkacin bakinsu, game da matakin da Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya ɗauka, na raba motocin alfarma, ga membobin majalissar dokokin jihar, duk kuwa da halin matsin rayuwar da al’umma ke ciki.

Tun da farko dai, Gwamna Idris, ya sanar da raba motocin ne, ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya na mai cewar, “na ɗauki hakan a matsayin wani mataki na cika alƙawarin da muka ɗaukarwa al’ummar jihar Kebbi na hidimta musu”.

“Ina mai farincikin cika alƙawarina, na raba motoci guda 24 ƙirar Toyota Jeeps, ga jajirtattun ƴan majalissar dokokin jihar Kebbi, domin yabawa irin ƙwazon da su ke nunawa.

“Yau, a gidan gwamnatin jihar Kebbi, da ke Birnin Kebbi, Ni da Kaina na miƙa waɗannan motoci ga ƴan majalissun, tare da yaba musu kan irin haɗin kan da su ke bamu, gami da fahimtar junan da ke tsakaninmu. Babu shakka alfanun da ke cikin haɗin kai tsakanin ɓangaren zartaswa da na majalissa ba ƙarami bane. Domin ƙara bayyana wannan haɗin kai kuma, ni da kaina na bi sahun Shugaban Majalissar Dokokin, Rt. Hon. Usman Muhammad Ankwe, wajen ɗana tuƙin tasa motar da ya rabauta da ita”.

Sai dai, lamarin bai yiwa da dama daga cikin masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani daɗi ba, inda su ke cigaba da ƙalubalantar lamarin, duba da irin halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki, gami da yunwa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button