Rahoto : Gidajen Mai Na Sayar Da Litar Man Fetur Kan Naira 560, A Kano
An samu ɓullar dogayen layuka a gidajen man ƙwaryar birnin Kano, ya yin da sayen man ke cigaba da zama gagarumin Aiki, ga mazauna jihar.
Wannan yanayi kuma ya zo ne, bayan da sabon shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da cire tallafin mai, a ya yin da ya ke gabatar da jawabinsa na ranar rantsuwa.
A wani zagayen kuturunka nawa da wakilin RARIYA ONLINE, Miftahu Ahmad Panda, ya gudanar a birnin Kano dai, ya gano yadda ɗai-ɗaikun gidajen man da ke buɗe su ke sayar da feturin a sama da Naira 500, ya yin da da dama kuwa suka kasance a garƙame.
Wanda hakan ya sanya motoci da dama su ka kasance akan manyan layukan sayen feturin, baya ga waɗanda su ke komawa saye, a wajen masu bunburutu.
A wani gidan mai, da wakilin namu ya halarta, da ke kan titin Ring Road dai, ya iske yadda Jami’an hukumar kula da Albarkatun Man fetur ta ƙasa (DPR) su ka mamaye gidan, tare da korar dukkannin mutane da ababen hawan da su ke ciki, da ma garƙame gidan, bayan samunsu da laifin sayar da manfetur ɗin akan farashin Naira 560.
Su ma masu sayen man a ire-iren waɗannan gidajen mai sun koka, kan yadda man ya zama lu’u-lu’u cikin kwana guda, Inda Ahmad Jafar, da ke gudanar da sana’ar caji, a unguwar Ja’en Sabere ya bayyana wa wakilin Rariya Online, Miftahu Ahmad Panda, cewar haƙiƙa tsadar man na cigaba da jawowa sana’ar su koma baya.
Shima wani matuƙin baburin Adai-daita sahu, ya bayyana mana cewar, tuni su ka ɗage farashin kudaden da su ke karba a hannun Jama’a, sakamakon tsadar man.
Sai dai, dukkannin ƙoƙarin Jaridar Rariya Online, na ji daga bakin mahukunta kan ko me yasa aka haihu a ragaya, abin ya ci tura.
Rahoton Jaridar : ©Rariya Online – Matatar Labarai 2023