Rahotanni

Rahoto : Kasuwancin Fitar Da Kayan Noma Na Cigaba Da Haɓɓaka, a Najeriya

A baya dai, al’ummar Najeriya sun sha tafka asara, sakamakon gaza fitar da kayayyakin da su ke nomawa, sai dai a yanzu labarin ya sha ban-ban, bayan da kayayyakin noma da dama su ke samun gwagwgwaɓan tagomashin fitarwa zuwa ƙasashen Turai, Amurka, yankin Asia, da ma sauran ƙasashen Afirka.

Wata ƙididdiga da aka fitar ta kuma bayyana yadda kayayyakin na noma da aka samar daga Najeriya ke cigaba da taka rawarsu da tsalle, a nan kusa. A ƴan shekarun nan dai, kayayyakin noman da aka samar a Najeriya su na cigaba da samun tagomashin fita, zuwa yankin Turai, Amurka, da ma Asia.

Ƙididdiga dai, ta tabbatar da cewar kaso 80 na kayayayyakin da ke da jiɓi da noma, da ake amfani da su a ƙasashen yankunan, sun fita ne daga Najeriya.

Fitar da kayayyakin noman da ke cigaba da ƙaruwa cikin shekaru biyar kuma, ya fi gwaɓi ne, a shekarar 2022, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasa, ta bayyana.

Rahoton hukumar, ya kuma hakaito yadda kayayyakin noma da su ka kai kimar Naira biliyan 598.2 ya kasance an fitar da su ne, a shekarar 2022, wanda ke nuna ƙaruwar kaso 18.5 idan aka kwatanta da alƙaluman da aka fitar, a shekarar 2021. Hakan kuma ya zama wani babban jigo da ya sanya sha’awar al’ummar Najeriya da dama, akan kasuwar fitar da kayayyaki.

Babban abin sha’awar dai, shi ne yadda ƙasashe a yankin Turai, su ka samar da muhimman kasuwanni ga masu fitar da kayayyakin daga Najeriya.

Ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ta nuna kan harkar ta fitar da kayayyakin noma kuma, ita ce ta kasance ummul aba’isin haɓɓakar fitar da kayayyakin zuwa ƙasashen duniya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button