Rahotanni

Rahoto : Mummunan Halin Da Makarantar Firamaren Ashuran Chiroma Ke Ciki, A Jihar Jigawa

Da safiyar yau (Alhamis) ne, wakilin jaridar Rariya Online, Usman S Idris, ya kai ziyara makarantar firamaren Gwamnati ta Ashuran Chiroma, da ke ƙaramar hukumar Kafin Hausa, ta jihar Jigawa, domin tsinkayen halin da ta ke ciki.

Inda kuma ya iske makarantar na fuskantar ƙalubalen ƙarancin ruwan sha

Wakilin namu, ya samu zarafin zantawa da Shugaban Malaman makarantar (Head Master) tare da wasu daga cikin Ɗalibai, inda su ka shaida masa irin halin da makarantar ke ciki, kan matsalar ruwan da su ke fuskanta, a wannan Makaranta.

Inda su ka ce hatta ruwan sha ma wahalar samu ya ke musu, a wannan makaranta, ballantana kuma ruwan yin tsarki da yara ke amfani da shi bayan kammala fitsari, ko bayan gida.

Ka zalika, shugaban Malaman na wannan makaranta ya kuma shaidawa wakilin namu cewar, sun kai ƙorafi ga hukumar da ke da Alhakin kula da matsalar, sun kuma zo sun gyara musu famfon da su ke amfani da shi, a karon farko, Sai dai gyaran ko kwana biyu bai yi ba, ya sake lalacewa, sun kuma sake kai ƙorafi a karo na biyu, amma ko zuwa a duba matsalar ba a yi ba, ballantana a yi zancen gyara.

Shugaban Malaman ya kuma koka kan yadda matsalar ruwan ke kawo musu cikas ga karatu, duba da yadda ana tsaka da ɗaukar darasi yara ke tafiya shanruwa, kuma dole ake barinsu su tafi domin samowa a wasu wuraren.

Suma wasu daga cikin ɗaliban wannan makaranta, sun bayyana yadda su ke ƙaunar ɗaukar darussa, amma ƙishin ruwa ke takura musu, har ta sanya dole su haƙura su tafi neman inda za su samu ruwan sha.

A ƙarshe shugaban Malaman makarantar, ya roƙi hukumar da lamarin ya shafa, da ta taimaki wannan makaranta tasu, duba da yanayin da su ke ciki.

Sai dai, dukkannin ƙoƙarin Jaridar Rariya, na taɓa-alli da hukumar Ilimin bai ɗaya ta jihar, da ma hukumar samar da ruwan sha, ya ci tura, kawo lokacin da muka kammala tattara wannan rahoto.

Daga : Usman S Idris.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button